Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar SSS ta Cafke Wasu da Tace Su ne Suka Sace Yaro Dan Shekara Bakwai a Kano


'Yansanda
'Yansanda

Makon da ya wuce ne wasu suka sace wani yaro yayin da suka bukaci a biyasu nera miliyan goma kafin su sakeshi amma daga bisan sun kashe yaron.

Tun lokacin da aka sanarda sace yaron dan shekara bakwai da haifuwa jami'an tsaro suka shiga neman wadanda suka yi aika aikar.

Shugaban hukumar SSS reshen Kano Mr. Etang ya bayyana yadda jami'ansa suka cafke wadanda ake zargin sacewa da kashe yaron dan shekara bakwai. Ranar hudu ga wannan watan suka sace yaron. Mr. Etang yace hukumomin tsaro sun gano cewa wasu suna anfani da wasu sabbin hanyoyin satar mutane da neman a biyasu dimbin kudi. Wato sun mayarda lamarin wata sana'a.

Yace sakamakon rahotannin siri dake hannunsu sun kama wasu mutane da suke tuhuma da satar wani yaro dan shekaru bakwai. Yace bincikensu ya nuna cewa wani mai suna Sarki ne ya shirya yadda za'a sace yaron da kuma ranar da za'a sace shi da hadin baki da wani mai suna Aliyu Muhammed.

Bayan sun sace yaron sai suka yi masa wata allura wadda ta kaiga mutuwar yaron.

Aliyu Mohammed ya kara haske yadda ya samu ya sace yaron bayan da maigadansa ya nuna masa yaron. Dama yaron na zuwa gidan maigidan Aliyu sayen alawa. Ganin haka sai ya ba Aliyu nera dubu daya ya dinga sayawa yaron alawa har su saba. Ya fadawa Aliyu cewa bayan sun saba sai ya kawo masa yaron a wata makaranta. Aliyu ya kwashi wajen makonni uku yana sayawa yaron alawa har sai da ya saba dashi. Bayan ya mika yaron ga maigidan nasa sai ya sa Aliyu ya rubuta wasika ta fadawa iyayen yaron cewa ya bata.

Daya daga jikin mutanen Jilili Muhammed shi ya yiwa yaron allura wadda ta sa hankalinsa ya gushe kafin daga baya ya mutu. Maigidan nasu yace bayan an ba yaron allura sai ya karbeshi. Har zuwa magariba yaron yana nunfashi amma da gari ya waye sai suka gani yaron ya mutu.

Tun da suka cafke yaron suke waya da baban yaron kan kudin da suke bukata kafin su saki yaron.

Umar Muhammed shi ya bada lambar asusun bakinsa inda baban yaron aka fada masa ya saka kudi har nera miliyan biyu. Amma Umar yace shi a Kaduna yake Aliyu kuma kaninsa ne shi yace ya bashi lambar asusun bankinsa. Aliyu ya fada masa cewa abokinsa ne zai aiko masa da kudi. Yace tunda ya aikamasa da lambar bai sake jin wani abu ba sai biyar ga wannan watan ya ga kudi ya shigo masa. Yace shi bai san ko nawa ne kudi ba. Da ya nunwa wansa sai yace nera dubu biyu ne. Da ya kira Aliyu yace an tura masa dubu biyu sai Aliyu yace a'a nera miliyan biyu ne. Umar yace shi bai san abun dake faruwa ba sai da aka kamashi.

Mr Etang yace zasu gurfanar da mutanen a gaban kuliya domin su fuskanci hukunci.

Ga rahoto.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG