Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Najeriya Ya Gargadi UNICEF Ya Sanar Da Hukumomi Kafin Horar Da Ma'aikatarsa


Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai
Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai

Ma’aikatar sojin Najeriya ta dage haramcin gudanar da ayyuka da ta dorawa asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) wato UNICEF dake aiki a arewa maso gabashin kasar.

Sojojin un bada sanarwar ce sa’o’i bayan dakatar da ayyukan asusun bisa zarginsa da yiwa kungiyar ‘yan bindiga leken asiri a yankin da ya sha fama da matsalolin ta’addanci.

Da safiyar jiya Juma’a ne ma’aikatar sojin Najeriya tace ta tattara wasu bayanai masu inganci dake tabbatar da wasu ma’aikatan asusun yaran na MDD, yana dauka kuma yana horar da masu leken asiri da zasu taimakawa ‘yan ta’addan Boko Haram da magoya bayansu. Ma’aikatar sojin tace zata dakatar da ayyukan UNICEF tsawon watanni uku.

Da yammacin jiya Juma’ar ne kuma jami’an sojojin kasar suka gana da wakilan UNICEF wanda daga bisani suka sanar da dage takunkumin. Mai magana da yawun sojan Najeriya Onyema Nwachukwu yace jami’an sojan sun fadawa wakilan UNICEF cewa su daina gudanar da ayyukan da zasu kawo matsala ga tsaron kasa da kuma yaki da ake yi da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Ma’aikatar sojin ta gargadi ma’aikatan UNICEF da su sanar da hukumomin da suka dace a duk lokacin da suke niyar su dauki ko su horar da sabbin ma’aikatansu a nan sansanin sojan.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya da ya sha fama da rikicin ‘yan ta’adda, ya zama tamkar babbar tungar kungiyar Boko Haram, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu talatin, kana wasu dubun dubata suka arce daga gidajensu. Rikicin ya haddasa tsananin bukatar kayan taimako a yankin na kogin Chadi kana ya bar galibin yankin da dogaro da taimako daga kasashen waje.

Kungiyar kasa da kasa ta Amnesty ta yi Allah wadai da dakatar da ayyukan UNICEF na jiya Juma’a, tana mai cewa wannan wani mataki ne na tsorata kungiyoyin agaji da na kare ‘yancin bil adama na kasa da kasa da suke aikin ceto rayukawr jama’ar dake yankin da yaki daidaita.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG