Yayin da ‘yan siyasa a Najeriya da jam’iyyun su ke daura damarar fafatawa a babban zaben kasar da zai gudana a watan fabarerun badi, masu ruwa da tsaki a fagen siyasar kasar na ci gaba da fashin baki dangane da yadda akida da tsarin uban gida a harkokin siyasar kasar.
Siysar uban gida a najeriya, wani al’amari ne dake ci gaba da daukar sabon salo a kasar.
Yadda jam’iyyu APC da PDP suka gudanar da zabukan fitar da gwani na ‘yan takarar gwamna dana ‘yan majalisar dokoki da kuma korafe korafen da suka biyo baya ya kara haska mummunan tasirin sisayar uban gida a najeriya.
Zaben fitar da ‘yan takarar gwaman Lagos a Jam’iyyar APC dana jihar Kano a jam’iyyar PDP na daga cikin dinbin misalan yadda jam’iyyun suka yi zabukan su na cikin a bana. Abinda masu kula da lamura suka ce zai iya haifar da gagarumar matsala nan gaba, ganin yadda sau da dama wadanda ake kira “uban gida” suke dagewa kan wanda suke so, ko da kuwa jam’iyar da kuma sauran magoya bayanta basu ra’ayinshi.
Da damai dai ‘yan najeriya na cewa, siyasar uban gida na daga cikin manyan dalilan dake hana ‘yan majalisar dokoki ta kasa tabuka abin kirki a zauren majalisar.
Saurari Cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari
Facebook Forum