Kungiyar ta cimma wannan kuduri ne a wani gagarumin taro da ya samu halartar matasan na “CAN” daga dukkan sassan arewacin Najeriya.
Shugaban kungiyar Mai Bushara Musa Misal ya nesanta addini da daukar doka a hannu ya na mai cewa zama lafiya ya fi zama dan Sarki.
Shi ma tsohon shugaban matasan kiristoci na Najeriya Fasto Simon As Dolly ya tuno dabi’un zaman lafiya na marigayi Sarkin Adara da masu satar mutane su ka kashe a Kaduna da kira ga matasa su rike zumunci irin na marigayin ba tada kura a duhun kai ba.
Taron ya samu halartar matasa mata da ma dattawa da su ka taya matasan fitar da bayanan bayan taro masu ma’ana ciki kuwa har da Fasto Paul Gwaza da sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha.
Tattaunawa tsakanin kungiyoyin mabiya addinin kirista da musulmi a lokacin da a ke tinkarar babban zabe na da muhimmanci don barin hukuma ta zama mai daukar hukunci ba mutane masu bambancin ra’ayi ba.
Ga rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Abuja, Nasiru Adamu El-Hikaya:
Facebook Forum