Wanan dokar zabe da majalisar dattawa ta amince da ita tana kunshe ne da muhimman batutuwa da hukumar zabe za ta yi amfani da su a zabe mai zuwa.
Abubuwan da suka fi daukan hankali guda biyar ne, akwai batun na'urar tantance masu kada kuri'a ,da ranar kammala zaben fid da gwani, da tanadi game da cire alamar jam’iya ko dan takara, adadin kudin da za a kashe a yakin neman zabe da kuma hukuncin dauri idan an samu mutum da katin zabe na jabu ko kuma na wani daban ba nashi ba.
Bisa ga bayanin da aka yiwa Sashen Hausa a kan wannan doka, idan ba a kawo kad rida ba har tsawon sa'o'i uku kafin a fara zabe, to sai a daga wanen zaben sai washe gari. Duk gyaran da ya kamata a yi a dokar an yi har da maganan zaben fid da gwani. Dole ne a kamalla su kwanaki 90 kafin zabe. Akwai maganar alamar jam’iya da kuma duk wanda aka kama da katin zabe na jabu za a daure shi shekaru biyar a gidan kaso,wanda kuma ya zo da katin wani za a daure shi shekara biyu. An kuma soke maganar rajistar masu kada kuri'a a dokar. Idan babu kad riba babu zabe.
Majalisar dattawan ta yi fatan shugaba mohammadu Buhari zai ratabba hannu a dokar ganin cewa sau uku yana mayar wa majalisar da ita ba tare da ya sa hannu ba, dai dai ‘yan majalisan sun ce gyare gyaren da aka yi zai kara inganta demokradiyar kasar.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda
Facebook Forum