Tare da yin taka-tsan-tsan, shugabanin kasashen Yammacin duniya, sun yi tsokaci kan gwajin makamin nukiliyan nau’in Ballistic mai tafiyar matsakaicin zango da Iran ta bayyana ta yi nasarar yi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter a jiya Asabar cewa “Iran ta yi gwajin makami mai linzami nau’in Ballistic, wanda zai iya kai wa ga Isra’ila, suna kuma aiki tare da Korea ta arewa, matsayar da aka cimma ba ta da amfani.”
Shugaba Trump yana nuni ne da matsayar da aka cimma a shekarar 2015, wacce ta ba da dama aka dagewa Iran takunkumin tattalin arzikin da aka saka mata, domin ta daina shirin gina makamin na nukiliyan.
Kasar Faransa ma, wacce tare da ita aka cimma matsayar, ta maida martani a wata sanarwa da ma’aikatar harkoki wajenta ta fitar, inda ta nemi Iran da ta dakatar da duk wani aiki da zai iya haifar da tarzoma a yankin.
Isra’ila ma, wacce kusan ita ce kasar da koda yaushe Iran ta fi maida hankalinta akai, ta bayyana gwajin makamin a matsayin “tsokanar” Amurka da Isra’ila da sauran kawayenta da fada.
Facebook Forum