Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Yan Gudun Hijira Dake Tsallakawa Turai Na Kara Karuwa


Wasu yan gudun hijira dake tafiya daga Turkiyya zuwa Girka.
Wasu yan gudun hijira dake tafiya daga Turkiyya zuwa Girka.

Shugaban Majalisar Kasashen Turai Donald Tusk yace, har yanzu yawan ‘yan gudun hijirar da ke ketarawa ta kan tekun Aegean daga kasar Turkiyya zuwa kan iyakokin kasashen Turai sun ninninka, wanda hakan yasa akwai bukatar shawo kan lamarin.

Da ya ke jawabi jiya Alhamis ga Manema labarai a taron da Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ke jibinta a birnin Ankara, Mista Tusk yace, idan aka fara maida bakin hauren zuwa kasashen da suka fito, hakan zai karya lagon kasuwancin masu hada-hadar safarar mutanen da suke ketararwa ta ruwa zuwa Turai.

Shugaban ya yanawa Turkiyya game da hobbasarta na dada tsuke kan iyakarta da kuma sake tsaurara matakan samun Visa don ganin ta taimaka wajen shawo kan lamarin kwararar ‘yan gudun hijirar.

Shima Firaministan Ahmet Davutoglu ya fadi cewa, kar dama a yi zaton cewa Turkiyya da Girka su kadai za su iya jurewa matsalar kwararar bakin hauren da suke tururuwa zuwa Turai a kullum.

Dama Donald Tusk din ya gargadi hatsarin kwararar bakin a lokacin da ya taba ganawa da Firaministan Girka Alexis Sipras.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG