Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Yan Gudun Hijira Dubu 14 Suna Makale Kan Iyakar Girka Da Macedoniya


Yan Gudun Hijira a bakin iyakar Girka.
Yan Gudun Hijira a bakin iyakar Girka.

Dubban ‘yan gudun hijira har yanzu suna makale a kan iyakar Girka da Macedoniya, yayin da shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai suke shirin ganawa da takwarorinsu a Turkiya domin tattaunawa kan matsalar a wani taro na gaggawa da za a gudanar yau Litinin.

Shugabannin kasashen Turai zasu yi kokarin matsawa Fara Ministan Turkiya lamba ya rage yawan ‘yan gudun hijiran dake kwarara kasashen Turai su koma mayar da wadanda basu cancanci a basu mafaka ba a kasashen.

Kimanin ‘yan gudun hijira dubu 14 ne a halin yanzu suka yada zango a kan iyakar Girka da Macedoniya, da fatar za a kyalesu su nufi Arewaci. Sai dai kasashe da dama da suka gwammace tafiya kamar Jamus da Scandinavia, sun sake gabatar da tsarin sa ido kan iyaka, wani abu dake barazana ga harkokin sufuri da cinikayya a kasashen da ba a bukatar bisa.

Yayinda ake kyautata zaton karuwar ‘yan gudun hijiran idan sanyi ya ragu, shugabannin kasashen kungiyar tarayyar turai suna zubawa fara ministan Turkiya Ahmet Davutoglu ido a shawo kan kwararar ‘yan gudun hijirar.

Sai dai Turkiya tana fama da tata matsalar kwararar ‘ya gudun hijirar, kasancewa ta tsugunar da sama da mutane miliyan biyu da suka kauracewa Syria inda ake fama da tashin hankali.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG