Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matafiya A Najeriya Na Cigaba Da Kokawa Kan Tsadar Kudin Mota Duk Da Tallafin Gwamnati Na Kaso 50%


Wata tashar mota a Abuja
Wata tashar mota a Abuja

“Gaskiya al’amarin yanzu fa sai ahankali, da muna biyan N500 daga Abuja zuwa Nasarawa amma yanzu kudin ya nunka zuwa N2000, wallahi muna wahala! In kazo da kaya ko mai kankantar su suma a ce sai ka biya kudin su.” inji Fidelis

A daidai lokacin da bukukuwan kirsimeti ke karatowa, bisa al’ada jama’a da dama ne ke tururuwa zuwa tashoshin motoci a birnin Abuja domin tafiya zuwa jihohinsu daban-daban domin hutun karshen shekara, ziyara da bikin kirsimeti.

Amma sai dai a wannan shekara abin yasha ban-ban, ko mai ya janyo haka?

Fidelis matafiyi ne da zai je Nasarawa domin bikin kirsimeti da hutun karshen shekara, amma yana kokawa da irin ninki na tsadar kudin mota da ake ta samu, musamman a wannan lokaci na shirin bukukuwan karshen shekara duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasa.

“Gaskiya al’amarin yanzu fa sai ahankali, da muna biyan N500 daga Abuja zuwa Nasarawa amma yanzu kudin ya nunka zuwa N2000, wallahi muna wahala! In kazo da kaya duk kankantasu suma a ce sai ka biya kudin su.” inji Fidelis

Da mukaji ta bakin direbobi, kan musabbabin karin kudin da matafiyan suke fama dashi, Malam Nuhu direban mota ya shaida mana dalilin karin wanda yana da alaka da karin kudin man fetur da ake fama dashi a kasa sakamakon cire tallafin na mai.

Malam Nuhu yana cewa “babban musabbabin banbanci na farashin kudin mota da ake fama dashi shine man fetur da yayi tsada. Da can in munyi lodi zamu sami kudin da zamu ajiye da wanda zamuyi hidimar iyalanmu, to amma yanzu za kaga ga kudi nan mai yawa amma kuma kusan duka yana tafiya a sayan mai ne, fasinja ma yanzu sunyi karanci saboda tsadar rayuwa da rashin kudi a hanun mutane”.

A baya-bayan nan gwamnatin ta sanar da tallafin kudin sufuri da kaso 50% cikin dari ga illahirin matafiya har na tsawon wasu kwanaki, domin samar da rangwame ga matafiyan, a wani taron manema labarai ne Ministan Ma'adinai, Dele Alake, ya shaida haka, inda ya jaddada kudirin shugaban kasa na ganin ya rangwanta ma al’umma da saukaka masu musamman a irin wannan lokaci da mutane na da bukatar tafiye tafiye don bukukuwa da hutun karshen sheka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG