A ranar 25 na kowane watan Disamba ake gudanar da
bukukuwan Kirsimeti a fadin duniya, domin tunawa da ranar
haihuwar Yesu Almasihu.
Duk da yadda ake raya bikin a yankin Turai, wasu Kiristoci ‘yan Afrika mazauna Jamus sun ce, lokaci ne da ke saka su kewar gida saboda banbanci a tsarin gudanar
da bikin a Turai.
A kasashen Afrika da dama Kiristoci dai na raya ranar Kirsimeti da soma zuwa mujami’u don yin addu’o’i a safiyar ranar.
Daga bisani a dawo gida a soma hidindimu na girke-girke da
rabe-raben abinci ga makwabta da kai ziyara ga ‘yan uwa da
abokan arziki da dai sauransu.
Amma a Jamus kamar sauran kasashen Turai, ana kai wa
kololuwar shagulgulan ne a jajiberin bikin Kirsimeti inda ake
musayar kyaututuka a tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki da
kuma liyafar cin abinci a cewar Herr William Schaff.
Wannan tsarin duk da armashinsa ga Turawan yayi hannun riga da al’adar shagulgulan Kirsimeti na ‘yan Afrika kamar yadda wasu ‘yan Afrika mazauna Jamus suka sheda wa Muryar
Amurka.
Wannan yanayi dai, na sanya da dama daga cikin ‘yan Afrika
kewar gida a lokacin shagulgulan da ke da matukar
muhinmanci ga mabiya addinin Kirista, wasunsu na iya kokari
don ganin sun debe wa kansu kewa, kamar hada liyafar cin
abinci da nishadantar da kansu a wannan rana.
A saurari rahoton Ramatu Garba Baba daga Birnin Bonn:
Dandalin Mu Tattauna