Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya gana da shuwagabanin kungiyoyin addini inda ya bukaci gudunmuwarsu wajen neman hanyoyin warware matsalar tsaron da ta addabi kasar da makwaftanta.
Sanin mahimmancin gudunmuwar shugabanin addinai wajen warware matsalolin da suka addabi jama’a ko wacce iri ce ya sa shugaban kasa Mohamed Bazoum kiran wannan taro domin sanarda malamai abubuwan da ake jira daga garesu akan batun zaman lafiya a wannan lokaci na fama da matsalar tsaro domin ‘yan magana na cewa ko kana da kyau ka kara da wanka..
Awoyi a kalla 2 aka shafe ana wannan tantauna kuma a cewar Shugaban kungiyar jama’atul izalatul bidi’a wa ikamatus sunnah Souleyman Maman gamsuwa da irin bayanan da suka ji daga wajen shugaban kasa abu ne da ya kara basu kwarin gwiwar ci gaba da aiki.
Samun hadin kan al’umma a wannan tafiya ta karfafa matakan zaman lafiya abu ne da ya zama wajibi inji malamai.
Da ma dai a makon jiya shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yi irin wannan ganawa da sarakunan gargajiya da hakimai inda ya bukaci gudunmowarsu wajen fadakar da talakkawa nauyin da ya rataya a wuyan kowane dan kasa a kokarin samo bakin zaren tashe tsahen hankulan da ake fuskanta can da nan a wasu sassan kasar inda ‘yan ta’adda da barayin dabobi da masu satar mutane suka hanawa bayun Allah barci duk da irin jajircewar da jami’an tsaro ke yi akan wannan masifa dare da rana.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: