A wannan makon a shirinmu na matasa da siyasa a yau mun samu zantawa da Mal. Sagir Abdu Waziri, matashi wanda ya yi mana fashin baki dangane da dabi’ar da akan samu shugabanin da ita na cin hanci da rashawa, da kuma illar da hakan ke da shi ga yanayin dimokaradiyya.
Mal. Sagir ya ce wannan kalubale ne ga matasa da za su tantance irin jagororin da ya kamata su zaba, da kuma idan sun tsincin kansu a yanayi na shugabanci yaya ya kamata su rike dukiyar alummar da karantar yanayi na alummar da suka jagoranta.
Babban kalubale ne ga matasa da su zamo masu kishin kasa, tare da bukatar da a gudanar da bincike na tsanaki kuma mai zurfi dangane da zargin da ake yi wa gwamnan Jihar Kano, game da faifen bidiyon da ya fita na karbar kudi da ake zargin gwamnan jihar Kano da shi.
Mal. Sagir, ya ja hankalin shugabani da su zamo masu kishin kasarsu, da su yi koyi da irin tsarin mulki na wasu jihohin da ke Najeriya da wasu kasashen da ke makwabtaka da su wajen zama wakilan alummarsu.
Facebook Forum