Na fito da sabon salon kida da babu irinsa, wanda shi ba irin na larabawa ba kuma ba na 'yan kasar Tanzania ba, wanda ake amfani da na'urar Piano domin canza salon yadda ake waka da kida, inji mawaki Nura Ashraf.
Ashraf ya ce ya yi hakan ne ganin cewar mafi yawan fina-finanmu ana sanya waka da kida domin kawata fim tare da nishadantar da masu kallo.
Ashraf dai makadi ne kuma mawaki wanda yake kida na wakokin Hausa, kuma yana amfani da Piano. Wakokinsa sun fi maida hankali akan fadakarwa da nishadantarwa a fina-finan da ke fitowa.
"Shiga ta waka dai shi ne domin na kawo wani sabon abu, dabam ba kamar yadda aka saba ji ba a baya, duba da yadda waka ta sauya, ta hanyar amfani da sauti na kida tamkar yadda 'yan Tanzania ke yi."
A yanzu dai babu wani makadi da ya ke kida kamar irin na nasa, Ashraf ya bayyanawa DandalinVOA.
Abinda nafi buri bai wuce wakoki na, su taka rawa wajen kwatance ba mussaman ganin cewar ba kamar sauran mawaka ko makada nake salon waka ta ba, inji Ashraf.
Facebook Forum