Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AfCFTA: Ghana Zata Karbi Bakuncin Shugabannin Afirka 12 Da Manyan 'Yan Kasuwa A Taron Harkokin Cinikayyar Afrika


Nana Akufo Addo
Nana Akufo Addo

A karkashin jagorancin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, da babban sakataren harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afirka (AfCFTA) Wamkele Mene za a yi taron kan ci gaban Afirka karo na farko a Ghana. Taron da masu ruwa da tsaki suka ce Ghana da Afirka baki daya, za su amfana da shi.

Kamar yadda kungiyar ci gaban Afirka ta APN, wacce ta shirya taron ta bayyana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Accra, ana sa ran shugabannin Afirka 12 da manyan ‘yan kasuwa daga sassan Afirka da dama za su halarci taron da za a gudanar, ranar 26 zuwa 28 ga watan Janairun 2023. Shugabannin kasashen Najeriya, Kamaru, Cote d’Ivoire, Habasha, Kenya, Morocco, Afirka ta Kudu, Senegal, Guinea Bissau, Benin, Nijar, da Congo ne za su halarci taron.

Dakta Eugene Owusu, mai shirya taron kuma mai bai wa shugaban kasa shawara a kan ci gaban karni, ya ce taron zai zama wani dandali wanda shugabannin siyasa da 'yan kasuwa na Afirka zasu tattaunawa kan ci gaban Afirka, kuma taron zai kawo tsare-tsare da sauye-sauye don Afirka, da samun ci gaba a duk fadin nahiyar ta hanyar inganta hadin gwiwar tattalin arziki, zurfafa kasuwanci da zuba hannun jari.

Dr. Eugene Owusu
Dr. Eugene Owusu

Dakta Owusu ya kuma ce taken taron na AfCFTA “Daga Buri zuwa Aiki - Isar da ci gaba ta hanyar kasuwanci a nahiyar," na nuna irin gagarumar damar da AfCFTA ke bayarwa don zurfafa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da kuma ci gaban nahiyar baki daya.

Ministan yada labarai Ghana Kojo Oppong Nkrumah, wanda ya wakilci gwamnati a taron manema labaran, ya bayyana cewa muhimmancin taron bai misaltuwa domin dandali ne da za a samu haduwar ra'ayoyi masu karfi.

Taron Manema Labarai
Taron Manema Labarai

Tattaunawar za ta kasance kashi biyu; a ranar 26 zuwa 27 ga Janairu za a yi tattaunawar kasuwanci da harkokin shugabanci, sai kuma a ranar 28 ga watan Janairu shugaba Akufo-Addo zai jagoranci tattaunawa tsakanin shugabannin kasa, shugabannin masana'antu, da ‘yan kasuwa.

Masanin tattalin arzikin kasa Hamza Adam Attijjany, yace taron zai taimaka wa Afirka a bangaren kasuwanci, siyasa da tsaro.

Shi ko Issah Mairago Gibril Abbas, mai fashin baki kan al'amuran yau da kullum, ya jaddada muhimmancin warware bakin zaren harkokin kasuwanci a Afrika ta hanyar kasuwar bai daya da za a tabbatar.

Taron zai kuma samu halartar masana tattalin arziki, ma’aikatan banki, da sauran shugabannin ‘yan kasuwa a Afirka da ma wasu kasashe.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG