Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Taliban Ya Bukaci Zaman Sulhu A Afghanistan


Mayakan Taliban
Mayakan Taliban

Shugaban Taliban ya sake kira a nemi hanyar tattaunawa da Amurka domin kasar Afghanistan ta samu zaman lafiya saboda duka bangarorin suna shan wuya ne kawai

Shugaban Taliban dake Afghanistan,Hibatullah Akhundzada jiya Talata ya sabunta kiran da ya yi na ganin ya tattauna kai tsaye da Amurka domin ganin an kawo karshen yakin da ake yi, wanda zai baiwa kungiyar ‘yan yakin sa kai damar a tattaunawa dasu domin samun zaman lafiyan gwamnatin Kabul.

A cikin sakon sa na taya murnan bikin salla karama wanda za a yi bayan an kawo karshen azumin watan Ramadan, Shugaban na Taliban ya karfafa kemfe din da kungiyar tasa ta ke yi yana mai bada musali da ci gaba da kasancewar sojojin da Amurka kewa jagoranci da suka mamaye kasar.

Akhundzada yace muddin da gaske jami’an Amurka suke yi, lallai sunyi amanna da zaman lafiya musammam ganin an kawo karshen rikicin da ake yi a kasar to tilas ne su gabatar da kansu domin a hau teburin sulhu dasu domin ganin karshen wannan harin, harin da ya ce yana yiwa duka bangarorin biyu illa wato da sojojin Amurka da ma na Afghanistan din. Yanzu haka mutanen Afghanistan a shirye suke su rungumi batun sulhu.

Wadannan kalaman dai suna kunshe ne a cikin wata sanarawar da shugaban ya bayar ana kwanaki ukku a gudanar da bikin sallah wanda ake sa ran a yi ranar juma’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG