A cikin jawabi na minti shida ga Amurkawa, shugaban ya fada jiya Alhamis cewa, jami'ai masu yaki da ta'addanci, da sojoji, da sauran jami'an tsaro suna ci gaba da sa ido kan barazanar anan cikin gida da kuma ketare.
Idan har aka tabbatar da sahihiyar barazana, za'a sanarwa jama'a baki daya.Muna ganin yana da muhimmanci mutane ga yayinda suke gudanar da harkokinsu, su kuma sa ido," inji shugaban na Amurka.
Mr. Obama yayi magana ne bayan ya gana da shugabannin hukumomin tsaro na Amurka.
Ahalinda ake ciki kuma, majalisar dokokin Faransa jiya Laraba ta kada kuri'a fadada farmakin da kasar take kaiwa kan mayakan sakai na kungiyar ISIS, kungiyar data dauki alhakin hare haren da aka kai kan birnin Paris ranar 13 ga watan Nuwamba har suka halaka mutane 130.