Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kira Kasashe da Kungiyoyi Su Taimakawa Hukumar Cimaka Ta Duniya da Kudade


Mukaddashin Firayim Ministan Nijar, Bazu Muhammad, wanda ya jagoranci taron shi ne a tsakiya
Mukaddashin Firayim Ministan Nijar, Bazu Muhammad, wanda ya jagoranci taron shi ne a tsakiya

A wani taro da wakilan kasa da kasa da kungiyoyi, gwamnatin Nijar ta kira jakadun kasashe da wailan kungiyoyi su tallafawa hukumar cimaka ta duniya ko WFP da kudaden da zasu bata damar cigaba da ayyukan jinkai

Ita hukumar cimaka ta duniya ko WFP ta fara aikin jinkai cikin Nijar a shekarar 2015 domin mutane dari biyu da hamsin 'yan gudun hijiran Najeriya da suke tsugune a Diffa da mutanen da suka tsere daga kauyukan yankin saboda matsalar Boko Haram.

Baicin 'yan Najeriya dake Diffa akwai wasu 'yan Mali kusan dubu hamsin da su ma suka tsinci kansu a yankin Tilaberi sanadiyar rikicin 'yan ta'ada a kasar ta Mali.

Malam Bazu Muhammad mukaddashin firayim ministan Nijar yace mutanen suna bukatar agaji amma kuma sun lura tallafin yana raguwa daga masu hannu da shuni da kasashe. Yace ya kira ne ya nuna masu illar karancin tallafin da suke ba hukumar. Ya kira jakadun da wakilan da su yi rahotanni masu kyau domin samun tallafi.

Gwamnatin Nijar tayi taron neman wa hukumar abinci ta duniya tallafin kudi
Gwamnatin Nijar tayi taron neman wa hukumar abinci ta duniya tallafin kudi

Hukumar tana bukatan dalar Amurka miliyan ishirin da digo daya cikin gaggawa nan da zuwa watan Disamba na wannan shekarar ko kuma hukumar ta nade nata-i-nata.

A watan Disamban da ya gabata ne ita gwmnatin Nijar ta bukaci masu hannu da shuni su tallafawa 'yan gudun hijiran domin ayyukan jinkai na watanni goma sha biyu.

Saidai yawaitar hare-haren da yankin Diffa ya fuskanta na neman mayarda hannun agogo baya kamar yadda Hajiya Sa'adatu Barmo, shugabar hukumar jinkai ta kasar ta fada. Tace ana kokari kuma ana kan yin kokari amma abun baya isa sakamakon haren da ake kaiwa kan 'yan gudun hijiran. Tace idan an raba masu abinci yau ana iya kai masu hari kuma dole su gudu, su bar abincin su tafi wani wurin.

Karancin kudi ya tilastawa hukumar ta takaita taimakon da take bayarwa a asibitocin yara masu fama da tamowa. Matsalar kudin ta kai hukumar tunanen dakatar da ayyukanta a watan Disamba mai zuwa. Haka kuma hukumar zata janye tallafin abincin da take ba yara dake makarantun kwana kimanin dubu daya da dari biyu muddin masu hannu da shuni basu taimaka ba.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG