Batutuwan da shugabannin suka tattauna akai sun maida hankali ne akan barazanar ta’addanci da kuma habbakar tattalin arziki a kasar da ta fi yawan al’umma (kusan miliyan 200) a nahiyar Afrika.
Najeriya ta sami kanta cikin tarnakin ‘yan kungiyar boko haram masu tsattsauran ra’ayi, da suka kaddamar da gwagwarmayar su shekaru 9 da suka gabata da zummar kafa daular Islama irin tasu. Dubban mutane sun rasa rayukansu, an kuma sace daruruwan dalibai mata ‘yan makaranta, yayinda kungiyar tayi karfi ta kuma yadu har zuwa makwabtan kasashen Najeriya, inda ta kasance babbar barazana ga yankin yammacin Afrika a cikin ‘yan shekarun nan.
A shekarar da ta gabata gwamnatin Trump ta amince da saidawa Najeriya jiragen saman yaki na musamman, da wasu kayayyaki akan dala miliyan 600 don taimakawa dakarun Najeriya a yakin da suke yi da ‘yan boko haram, da mayakan ISIS, da kuma sa ido akan fasa kwabrin miyagun kwayoyi, da makamai, da kuma saffarar jama’a.
Facebook Forum