Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari Ya Kai Ziyara Jihar Cross Rivers


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ya kaddamar da manyan ayyuka biyu da suka hada da wani katafaren kamfanin samar da iri da sarafa shinkafa a jihar Cross River.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kai ziyara wuni guda jihar Cross Rivers dake yankin Niger Delta.

Shugaban ya kai ziyarar ce domin kaddamar da ayyuka na musamman guda biyu, da suka hada da bude asibitin mayakan ruwa da kuma bude wani katafaren kamfanin iri da kuma sarafa shinkafa.

Ziyarar ta jawo hankalin ‘yan jihar. Wani mai suna Sunday ya ce abun farin ciki ne domin karo na biyu ke nan da shugaban ya kai ziyara jihar kuma ya kawo masu ci gaba sosai musamman kaddamar da asibitin mayakan ruwa.

Shi kuma wani mutum mai suna Bassey, yace ziyarar babbar nasara ce garesu saboda kadamar da aikin noman shinkafa da shugaban yay yi.

A Bangaren gwamnati mataimakin gwamnan na musamman kan baki Barrister Musa Maigoro ya tabbatar da ayyukan da shugaban ya kaddamar.

A jawabin daya gabatar Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, yace kafa katafaren kamfanin samar da iri da sarafa shinkafa da gwamnatin jihar ta yi ya nuna cewa ta kama hanyar rage dogaro ga kason da take samu daga gwamnatin tarayya. Kazalika shugaban ya yi ga kira sauran jihohin Najeriya da su maida hankali akan noma domin inganta tattalin arzikinsu.

Farfesa Umar Aliyu na Jami’ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto masani akan harkokin noma, ya ce yanzu mutanen kudancin Najeriya sun soma gane mahimmancin rage dogaro ga mai. Sun soma ganin alfanun noma wajen bunkasa tattalin arziki.

A saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG