Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Masar Ya Yiwa 'Yan Jarida da Wasu Fursinoni Ahuwa


'Yan jarida biyu na Al-Jazeera dake cikin fursinonin da aka yiwa ahuwa
'Yan jarida biyu na Al-Jazeera dake cikin fursinonin da aka yiwa ahuwa

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya yi afuwa ga fursunoni 100 a jiya Laraba, ciki har da ‘yan jaridan nan guda biyu ma’aikatan gidan Talbijin na Al-jazeera, da ake zargi da yada labarun karya.

Daya daga cikin ‘yan jaridar kuma dan asalin Masar, Baher Muhammed yace, “Gaba daya mafarkin ya kare, yanzu zamu koma gidajen mu mu ci gaba da rayuwarmu.

Shi kuma daya dan jaridar dan asalin kasar Canada Mohammed Fahmy yace yana farin ciki, sannan zai ci gaba da fafutukar ‘yancin ‘yan jarida a Masar. Da an yanke musu hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari ne.

Bisa zargin labarun karya na goyon bayan gwamnatin Muslim Brotherhood ta tsohon shugaba Mohammed Morsi da sojoji suka hambarar a shekarar 2013 aka dauresu.

Cikin wadanda afuwar ta shafa har da fitattun masu fafutukar kare ‘yancin bil’adamar nan Yara Sallam da Sanaa Seif.

Afuwar ta zo a jajibirin Sallar Layya da yawanci shugabannin Misira kan yafewa fursunonin bisa dalilan rashin lafiya ko wani abu daban.

Sannan kwana 1 ya rage na halarta babban taron Majalisar Dinkin Duniya da shi shugaba El-Sisi zai je a birnin New York da ke nan Amurka.

XS
SM
MD
LG