Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Malawi Ya Yi Wani Zango Da Ma'aikata Mata Zalla


Ma'aikatan Jirgin Sama Mata Na Murna
Ma'aikatan Jirgin Sama Mata Na Murna

Kamfanin jiragen sama na kasar Malawi ya yi wani zango a tafiyarsa dauke da zallan ma'aikatan mata daga birnin Blantyre na kasar Malawi zuwa Dar-es-Salaam a kasar Tanzania.

Wannan ne karo na farko a tarihin sufurin jirgin sama na kasar Malawi da aka yi irin wannan zangon.

Mata ne suka gudanar da dukan ayyukan da suka shafi sufurin jirgin da suka hada da binciken matafiya kafin shiga jirgi, da kula da bukatun matafiya, da zaunar da matafiya a kujerunsu da kuma kula da tashin jirgi da abin da ya shafi harkokin sufuri a cikin jirgin.

Hatta jami’an da suke yin aiki a tashar jirgin saman da suka hada da ‘yan sanda da jami’an shige da fice, da jami’an kula da tashi da saukar jirgi a tashar mata ne.

Jirgin ya yada zango na sa’oi biyu a tashar kasa da kasa ta Kamuzu babban birnin kasar Lilongwe inda aka yi wani dan biki, inda uwargidan shugaban kasar Gertrude Mutharika ta gana da ma’aikatan jirgin.

Mutharika ta ce yanzu lokacin da ‘ya’ya mata za su yi tunanin cewa akwai wadansu fannonin da ba za su iya yin aiki ba ya wuce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG