A yau Juma’a, Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya rushe majalisar dokokin kasar sannan ya tabbatar da ranar da ake sa rai a watan Fabrairu mai zuwa domin gudanar da zabubbukan wuri, bayan rushewar gwamnatin Olaf Scholz a watan da ya gabata.
Rikicin cikin gidan da ya dabaibaye kawancen su Scholz a kan yadda za’a farfado da tattalin arzikin kasa mafi karfin arziki a nahiyar Turai ne ya janyo faduwar gwamnatin, sai dai wani mummunan harin da aka kai da mota ana tsaka da cin kasuwar Kirsimeti ya sabunta takaddamar da kasar ke yi a kan tsaro da matsalar bakin haure.
Da ya ke tabbatar da ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zabe, Steinmeier ya jaddada bukatar samun “kwanciyar hankalin siyasa” sannan ya bukaci a gudanar da yakin neman cikin mutunci da kyautatawa”.
Jam’iyyar CDU ta masu ra’ayin mazan jiya karkashin jagorancin Friedrich Merz ke kan gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kaso 32 cikin 100 tun kafin harin na makon jiya, kuma ta sha alwashin daukar tsauraran matakai a kan bakin haure tare da yiwa manufofin zamantakewa da tattalin arzikin kasar garanbawul.
Jam’iyyar da ke biye da ita a mataki na 2 ita ce AFD ta masu tsananin kishin kasa da kaso 19 cikin 100.
Dandalin Mu Tattauna