Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Hana Fitar Da Koko Zuwa Najeriya


Noman koko
Noman koko

Kamaru ta hana fitar da koko zuwa Najeriya, sakamakon kara da manoma koko a Kamaru su ka kai musamman a yakin kudu maso yammacin Kamaru.

A yayin wani taron rikicin da aka shirya a ranar 13 ga Yuni, 2023 a Yaoundé, Ministan Kasuwanci, Luc Magloire Mbarga Atangana, ya dauki mataki na hana fitar da kokon Kamaru zuwa Najeriya.

Shekaru da dama, masu gudanar da aikin noman koko na kasar Kamaru suna zargin 'yan Najeriya da fitar da kokon ta hanyar da ba ta dace ba musamman a yankin Kudu maso Yammacin Kamaru, wanda ke da doguwar iyaka da Najeriya.

Manyan motoci dauke da koko
Manyan motoci dauke da koko

Daga majiyoyin cikin gida a ma’aikatar kasuwanci, matakin da Minista Mbarga Atangana ya dauka ya biyo bayan ta’asar da ake tafkawa na fitar da danyen waken koko daga Kamaru zuwa Najeriya cikin ‘yan shekarun nan ta hanyar da bata dace ba.

Wannan lamari yana da matukar illa ga tattalin arzikin kasar Kamaru a cewar masana harkar kasuwanci da dama.

Buhunan Koko (Cocoa) n
Buhunan Koko (Cocoa) n

Edmond Kuate daya daga cikin masanan da suke sa ido kan wannan lamarin ya yi wa Muryar Amurka karin haske dangane da tasirin Koko ga tallatin arzikin kasar Kamaru.

“Koko na daga cikin kayan masarufi wadanda Kamaru tafi alfari da su. Musamman wajen kasuwanci da kasashen waje. Su ke baiwa Kamaru damar samun kudaden waje da kuma daidaita ma'auni na kasuwanci. A yayin da 'yan Najeriya suka yi amfani da hanyoyin damfara don samun koko daga Kamaru, a hakikanin gaskiya Najeriya ce take ribantuwa. Kuma kasar Kamaru na babbar asara. Hakan yana haddasa faduwar ma'aunin kasuwancin Kamaru”.

Edmond Kuaté ya kara da cewa “Wannan mataki ta Ministan Kasuwanci yana tunatar da mu cewar Kamaru da Najeriya kowannensu yana wakiltar kashi 6% na dukan kasuwancin koko da ake fitarwa a nahiyar Afirka. Sabanin Côte d’ivoire da Ghana da suke zakaru a wannan fanni. Saboda haka ya zama dole Kamaru ta kare muradunta a irin wannan yanayi”.

Wannan al’amarin ya dada karfafa musamman tun bayan barkewar rikicin ‘yan aware a yankunan Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yammacin Kamaru, a karshen shekarar 2016.

Saurari rahoton Mohamed Ladan cikin sauti:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG