Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Ya Soki Tashar Labaran Rasha


Sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kira tashar watsa labarai ta RT da Kremlin ke marawa baya, a matsayin tashar farfaganda, bayan tattaunawarsa gaba da gaba da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin.

Macron ya kira kafofin sadarwar kafofin farfaganda na bakantashi a zaben shugaban kasar da aka gudanar bana, a lokacin da ake ganin Putin yana goyon bayan ‘yar takara mai tsats-tsauran ra’ayi Marine Le Pen. Ana kuna alakanta kutsen hanyar sadarwar internet da aka yiwa ofishin yakin neman zaben Macron da Rasha.


Putin ya musanta zargin yayin wani taron manema labarai jiya Litinin a fadar Versailles, inda yace baiyi yunkurin shish-shigi a zaben kasar Faransa ba, duk da yake ya kare ganawarsa da Le Pen a watan Maris.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG