Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Kare Surukinsa Bisa Zargin Yunkurin Samar Da Kafar Tattauwa Da Rasha


Shugaban Amurka Donald Trump ya kare surukinsa kuma babban mai bayar da shawara a Fadar White House Jared Kushner, wanda kafafen yada labarai suka ce ya yi yinkurin samar da wata kafa ta bayan fage ta tattaunawa da jami'an Rasha, makonni kadan kafin Trump ya hau gadon mulki a watan Janairu.

Shugaba Trump ya bayyana cewa "Jared na babban aiki ga kasar," abin da ya gaya wa jaridar New York Times kenan da daren jiya Lahadi. "Na yadda da shi matuka. Kusan kowa na mutunta shi a yanzu haka ma yana kan aiki ne kan wani shirin da zai samar ma kasarmu biliyoyin daloli. Bugu da kari, watakila ma mafi muhimmanci, shi ne shi mutum ne na gari."

Kushner, dan shekaru 36 da haihuwa, wanda ya mallaki wani kamfanin harkokin gidaje da ke New York, kafin ya kasance daya daga cikin ma'aikatan Fadar White House, na auren Ivanka, diyar Trump, wadda ita ma mai bayar da shawara ce a Fadar ta White House.

Kushner, a cewar wasu kafafen yada labarai da dama, ya yi yinkurin samar da wata kafar sadarwa ta boye da Rasha, bayan da ya gana da Jakadan Rasha a Amurka Sergey Kyslyak, a farkon watan Disamba.

Wasu masu fashin baki kan harkokin waje sun ce wannan yinkurin da aka yi, yayin da saura makonni Shugaba Barack Obama ya bar gadon mulki, ya tayar masu da hankali saboda hakan na iya kawo cikas ga tsaron kasa, hasali ma wasu 'yan jam'iyyar Dimokarat sun ce kamata a janye shaidar tanancewa ta tsaro da aka bai wa Kushener.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG