Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Sake Gwajin Makami Mai Linzami


Koriya ta Arewa ta sake gwada wani makami mai linzami mai cin gajeren zango da safiyar yau Litini, yan kwanaki bayan da kungiyar kasashen masu arzikin masana’antu ta G-7 tayi kira ga Korea ta Arewa ta dakatar da shirinta na makaman nukiliya.

Rundunar sojan Amurka a yankin Pacific tace an gudanar da gwajin makamin ne a kusa da garin Wonsan a gabashin Korea ta Arewar. Rundunar tace ta bi diddigin makamin har na tsawon minti shida kafin ya fada tekun Japan, yanki da Japan kadai keda ikon wurin.


Rundunar tace wannan makami bai da wata barazana ga Amurka. Amma dai Firayi Ministan Japan Shinzo Abe, wanda ya fusata, ya sha alwashin mayar da martani.


Abe ya fada a gidan telbijin cewar zasu yi aiki tare da Amurka kuma zasu dauki takamaiman mataki na hana Korea ta Arewa.


Wannan ne karo na biyu da Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami a cikin mako guda duk da barazanan Karin takunkumi da MDD tayi da kuma Allah wadai da shugabanin kasashen kungiyar G-7 suka yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG