Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Dimokradiyar Kwango Ba Zai Halarci Taron Koli Na Kasashen Kudancin Afrika Ba


Shugaban kasar Dimokradiyar Kwango Joseph Kabila wanda ya ki mika mulki
Shugaban kasar Dimokradiyar Kwango Joseph Kabila wanda ya ki mika mulki

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen kudancin Afirka ko SADC zata bude taron kolinta yau amma shugaban kasar Dimokradiyar Kwango zai kauracewa taron saboda kin shirya zabe a kasarsa da kuma kin barin mulki duk da cikar wa'adinsa

Yayin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake kudancin Afrika, SADC a takaice, take shirin yin wani taron koli a yau Talata a kan yunkurin da jamhuryar Demokaradiyar Congo ke yi na shirya zabe da dedeta kasar, akwai yiwuwar shugaban Congon ba zai halarci taron ba.


Wani jami’in gwamnati ya fadawa Muryar Amurka cewa shugaba Joseph Kabila zai tura Firayim Minista Bruno Tshibala taron da za a gudanar a Luanda babban birnin Angola. Sai dai ofishin Kabila bai fitar da wata sanarwa ba a hukumance.


Martin Fayulu na hadakar jami’iyyun adawar DR Congo da aka fi saninsu da Ressemblement da turanci ya fadawa Muyar Amurka cewa, yakamata kungiyar kasashen kudancin Afrika ta fito karara ta fadawa Kabila ya sauka a kan mulki don kasar ta gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.


Hadakar jami’yyun adawa ta Ressemblement tana son ganin wata kungiya mai zaman kanta ta shirya zabe amma ba gwamnati ba, wanda hakan zai baiwa mambobinta kwarin gwiwar shiga zaben, cewa za a gudanar da zabe sahihi inji Fayulu.


Kungiyar raya tattalin arzikin kasashe da suke kudancin Afrika ta SADC a takaice, ta bude wani ofishi a birnin Kinshasa domin taimakawa kasar yayin da take tinkarar zabe cikin yanayin tashin hankali.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG