Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi matukar farincikin ganin yadda aka amsa kira game bukatar da ta gabatar ta a taimaka Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Lisa Schlein ta Muryar Amurka da ke wajen taron na Geneva ta aiko da rahoton cewa tuni aka yi alkawarin bayar da dala miliyan 528 na taimaka ma ‘yan Congo wajen miliyan 13 da ke fama saboda rikice-rikice da kuma raba da aka yi muhallansu.
Yayin da aka gudanar da tsaron na wuni guda, sai Shugaban bangaren kai dauki na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock ya shaida ma ‘yan jarida cewa an kama hanyar nasarar tara dala biliyan 1.7 din da aka bukata na agaza ma Janhuriyar Dimokaradiyyar Congon.
Facebook Forum