Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban China Ya Nemi a Kare 'Yancin Mata


Xi Jinping, shugaban China yayinda yake jawabi a Majalisar Dinkin Duniya
Xi Jinping, shugaban China yayinda yake jawabi a Majalisar Dinkin Duniya

A jawabin da ya yi a taron koli na Majalisar Dinkin Duniya shugaban China ya nemi duniya ta kara kaimi wurin kare 'yancin mata.

Shugaban kasar China (Shi) Xi Jinping, yayi kira ga shugabannin duniya da su kara kaimi game da kiyayewa da kare darajar ‘yancin mata. Ya fadi haka ne a taron Majalisar Dinkin Duniya game da daidaiton jinsin maza da mata.

Shugaban na Sin yayi alkawarin Dalar Amurka Miliyan 10 ga cibiyar matan ta Majalisar Dinkin Duniya, wanda kuma a daya bangaren masu fafutukar kare ‘yancin mata na ci gaba da sukar lamirin kasar saboda tsare wasu mata ‘yan gwagwarmaya.

Matan an kama su daga garuruwa daban daban ne a lokacin da suke kokarin rarraba takardun bayanai game da cin zarafin mata a tashohin sufurin ababen hawa na haya.

Daga baya kuma aka sake su bisa sa idon doka. Matan da suka halarci taron sun hada da Angela Makel ta Jamus da Ellen Johnson Sirleaf ta Laberia da kuma Firayim ministar Bangladesh Sheikh Hasina.

Shugabar Jamus ta yi amfanin da damar wajen bayyana bukatar kare mata daga matsalar fyade, cin zarafi da bautarwa, musamman a kasasehn Syria, Iraki, Najeriya da wuraren da ake rikici a duniya.

XS
SM
MD
LG