Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Ma'aikata 11 Daga Wata Mahakar Zinari a China


Mahaka 22 ne suka makale a karkashin kasa bayan wata fashewa da ta auku makonni 2 da suka gabata.

Masu aikin ceto a China sun fito da mahaka 11 da suka makale a wata mahakar zinari sakamakon wata fashewa da ta auku a ranar 10 ga watan Janairu.

Kafafen yada labaran kasar sun ce an fito da mutun daya daga mahakar da ke birnin Qixia a gundumar Shandong a gabashin kasar da safiyar Lahadi. An kai shi wani asibiti da ke yankin don jinya, amma ba ya cikin hayyacinsa sosai.

Wasu mahakan su 10, a wani bangaren mahakar dabam, su ma an fito da su daga karkashin kasa bayan da aka kasa su rukuni-rukuni tsawon sa’o’i. Sun iya samun damar magana da masu aikin ceto kafin ranar Lahadi kuma an kai musu abinci.

Jimlar mahaka 22 ne suka makale a karkashin kasa, mai zurfin kusan mita 600.

An samu rahoton mutuwar wani mutun daya cikin mahakan, yayin da har yanzu ba a san yanayin da sauran mahaka 10 suke ba.

Hukumomin China sun kama masu kula da mahakar da yawa, wacce har yanzu ake kan gina ta, saboda sun sanar da batun fashewar bayan sama da sa’o’i 24 da aukuwar ta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG