Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

James Comey Ya Caccaki Trump a Littafinsa


James Comey, tsohon shugaban hukumar FBI
James Comey, tsohon shugaban hukumar FBI

Caccakar da James Comey, tsohon daraktan FBI ya yi wa Shugaba Trump a littafinsa, ya sa magoya bayan shugaban sun kafa wani dandali a yanar gizo da zummar kare shugaban.

Magoya bayan shugaba Donald Trump na Amurka, suna shirin maida martani ta yanar gizo kan littafin tarihin rayuwar James Comey, da tsohon darektan hukumar ta FBI ya rubuta.

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar Republican, jiya Alhamis, ya kaddamar da wani shafi a internet da suka lakabawa suna LyinComey.com, wadda a ciki suka wallafa kalaman fitattun 'yan jam'iyyar Democrat suna sukar tsohon darektar na FBI a lokutan baya.Jam'iyyar ta Republican tana da niyyar bibiyar sahihancin littafin, kuma tayi amfani da shafin wajen nuna kare-rayi da sabani dake cikin littafin, kamar yadda tashar talabijin ta Fox ta bada labari.

Littafin na Comey mai suna "A Higher Loyalty: Truth, Lies and Leadership, da turanci, ranar Talata mai zuwa ake sa ran fara sayar dashi ga al'umma.

Kamfanin dillancin Labarai na Associated Press yace, Comey ya caccaki Trump, a zaman mutumin da bashi da da'a, wanda ba ruwansa da fadin gaskiya. Ya kwatanta shugabancin Trump,mai dogaro ko gudana kan tinkaho da jiji-da-kai da kuma biyayya sau da kafa kan gaskiya da kariya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG