Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Bukaci Kasar ta Soma Shirin Cirewa Iran Takunkumi


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

A jiya Lahadi shugaban Amurka Barack Obama ya umarci gwamnatin Amurka da ta fara shirin dagewa Iran takunkuman da aka kakaba mata.

Bisa abinda aka kira da ranar fara zartar da yarjejeniyar Nukiliyar Iran din da kasashen 6 masu fada aji suka kulla a watan Yulin da ya gabata.

Wannan fara shirin ne zai zama matakin farko na yin aikinda yarjejeniyar kamar yadda aka kullata. Obama ya fada a jiya Lahadin cewa,

“na yi maraba da wannan muhimmin matakin ci gaba, sannan mu da abokan huldarmu dole mu fuskanci mataki mai wahala na aiwatar da yarjejeniyar da ta hadamu game da shirin Nukiliyar Iran.”

Don tabbatar da cewa ba za a iya kera Nukiliya a wajen ba Kungiyar Tarayyar Turai ma ta mika kundin wa membobinta damar dubawa da kuma tsaida takunkuman.

A wata sanarwa a talbijin Iran din ta bayyana cewa, kasar zata cika sharuddanta, sannan ko a makon da ya gabata jami’an Iran sun ce, nan da karshen shekarar nan za su gama cika nasu ka’idodij.

XS
SM
MD
LG