Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Na Neman Hanyar Komawa Yarjejeniyar Cinikayya Ta TPP


Kwana hudu da kama mulki Trump ya caccaki yarjejeniyar cinikayya da gwamnatin Obama ta cimma da kasashen yankin Pacific da aka sani TPP ya kuma janye Amurka daga yarjejeniyar wadda yanzu ficewar kasar na yiwa manoma illa

Shugaban Amurka Donald Trump, a jiya Alhamis, ya umarci masu bashi shawara kan tattalin arziki da cinikayya su fara duba hanyoyin da Amurka zata sake shiga yarjejeniyar cinikayya kasashen da suke yankin Pacific da ake kira TPP a takaice, wadda ya janye Amurka daga ciki, kwanaki uku da kama aikinsa a zaman shugaban Amurka.

Wakilai da suke wakiltar jihohi da karfin su ya dogara kan aikin noma, a majalisar dokokin Amurka, sun ce bayan da suka kammala taro a fadar White House, kan cinikayya kan kayan amfanin gona, shugaba Trump ya gayawa mai bashi shawara kan harkokin tattalin arziki Larry Kudlow, da wakilin Amurka ta fuskar cinikayya Lighthizer, su auna fa'idar sake shiga yarjejenioyar da ake kira TPP a takaice, wacce gwamnatin Obama ta cimma.

Senata mai wakiltar jahar Nebraska, Ben Sasse, dan Republican mai sukar manufofin kasuwancvin gwamnatin Trump, yace, a yayin wannan taron shugaban ya juya ya kalli mai bashi shawara kan harkokin tattalin arziki Mr. Kudlow, yace masa "Larry, kaje ka tabbatar da an yi hakan."

Shi din Trump ya sha fadin cewa ya fi son yarjejeniya tsakanin kasa da wata kasa, maimakon hadakar kasashe, wadda a ganinsa ba'a yi wa Amurka adalci. Nan da nan dai babu tabbas kan kome yasa shugaban na Amurka ya sake shawara yake so ya maida A murka cikin wannan yarjejeniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG