Gidan rediyon gwamnatin Kenya, ya bada rahoton cewa an kori mataimakin shugaban kasar, George Saitoti, daga kan mukaminsa.
Gidan rediyon na Kenya ya bada rahoto a yau Jumma'a cewa shugaba Daniel Arap Moi ya kori mutumin da ya shafe shekaru 13 yana zaman mataimakinsa.
Mr. Saitoti memba ne na wata kungiyar da ake kira "Rainbow Alliance" ta wasu 'ya'yan jam'iyyar KANU mai mulkin kasar, wadanda suke yin adawa da take-taken shugaba Moi.
Gidan rediyon Kenya ya ce an kori mataimakin shugaban kwana guda a bayan da wani sahibinsa, mathews Adams Karauri, yayi murabus daga kan mukaminsa na karamin ministan ilmi. Har ila yau, Mr. Karauri ya canja sheka ya koma jam'iyyar adawa ta "Ford People Party."