Hukumomin kasar Kenya sun sako wata ba-Amurkiya da mijinta dan kasar Spain, a bayan da ta gano cewar babu wata alaka a tsakaninsu da hare-haren ta'addancin da aka kai kan 'yan Isra'ila a birnin Mombasa.
Har yanzu ana rike da 'yan kasar Somaliya su hudu, da 'yan kasar Pakistan su shida dangane da wannan lamari, amma hukumomin Kenya sun ce ba su gano wata alaka ba a tsakaninsu da kungiyar al-Qa'ida.
Masu bincike daga Isra'ila da Amurka suna tallafawa hukumomin Kenya wajen bin kadin wannan lamari. Jami'an Amurka suka ce lokaci bai yi ba na tabbatar da ko wanene ya kai hare-haren, amma kuma ana kara ganin alamun cewa watakila, wata kungiyar kasar Somaliya mai suna "al-Ittihad al-Islamiyya" mai alaka da al-Qa'ida tana da hannu a ciki.
A ranar alhamis, wata kungiyar da ba a santa ba mai suna "Rundunar Falasdinu" ta tuntubi 'yan jarida a Lebanon tana daukar alhakin kai harin.
Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya lashi takobin farauto wadanda suka kai harin na Kenya.