Haley, tayi magana da manem labarai na wani dan gajeren lokaci, bayan da ta halarci zaman kwamitin sulhu na farko tunda ta kama aiki. Amurka ce ta nemi a yi taron taron.
Ministan harkokin wajen Iran Javad Zariff, bai tabbatar ba kuma bai musanta cewa kasar tayi gwajin ba. Sai dai ya kara da cewa "makamai masu linzami ba sa cikin yarjejeniyar Nukiliya da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya ciki harda da Amurka. Ya ci gaba da cewa Iran, ba zata taba amfani da makamai masu linzami da ta kera cikin kasar wajen kaiwa wata kasa farmaki ba."
Shugaban Amurka Donald Trump ya kira yarjejeniyar Nukiliyar da aka kulla da Iran zaman wata "mummuna", har m,a a lokacin yakin neman zabe yayi barazanar zai yi watsi da ita.
A lokacinda Majalisar Dattijai take tantancetadomin wannan mukami jakadiyar ta Amurka Nikki Haley, ta kwatanta yarjejeniyat a zaman "mai kashe jiki ko gwuiwa" duk da haka tace zata fi maida hankali wajen ganin Iran tana mutunta sharuddan yarjejeniyar.