Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya Cika Shekaru 73 Yau


A yau ne shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekaru 73 da haihuwa, Tuni dai kafafen sadarwa suka fara taya shugaba Buhari murnar zagayowar ranar.

Tun bayan samun nasarar zama dan takara na jam’iyyar adawa ta APC gabanin zaben da ya lashe, batun mika ragama ga matasa, ko na shekaru, da rashin yin murmushi, da rashin lafiya da aka dinga yi sun ragu ko ma ace an daina. Ko babban Editan sashen hausa Aliyu Mustapaha ya taba yi masa tambaya akan shekarun sa da kuma tsayawa takara gabanin zaben shekarar 2011. Inda shugaban ya ce in ya kai shekaru 70 a duniya ba zai sake tsayawa takara ba sai dai in Allah Ne ya ba shi.

Magoya bayan shugaban na cigaba da jajircewa akan cewa har yanzu shugaban na da kuzarin yin aiki.

Mr Philip, wani jami’i ne da ke aiki a birnin tarayyar Abuja ya yi wa shugaban fatan Alheri ya kuma ce shugaban na da lafiyar da zai cigaba da gudanar da ayyukansa.

Shi ma Abubakar Ibrahim Dankurama yi kyakyawar fata ga shugaban, ya na mai cewa shekaru basu ne abin dubawa ba amma chanchantar mutum. Ya kuma ce a yadda ya ke gani, shugaba Buhari ko da ya kai shekaru 100 ba zai girgiza ba.

Kwanan baya shugaban matasa na jam’iyar APC Dasuki Jalo Waziri ya Chacchaki shugaban inda ya ce ya jingine matasa a gefe. Duk dai ya ce ba wai zai yi fito na fito da shugaban bane, zai ba jam’iyyarsa duk goyon bayan da ya kamata haka kuma suma matasan da ya ke wakilta ba zai ajiye su a gefe ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG