Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Samu Hunter Biden Da Laifi A Tuhume-Tuhume 3 Kan Amfani Da Bindiga

Hunter Biden
Hunter Biden

Mataimakan alkalin jihar Delaware 12 ne suka samu dan shugaban kasar da laifi a tuhume-tuhumen aikata manyan laifuffuka 3 dake da nasaba da saye da mallakar bindiga lokacin da yake yawan ta’ammali da hodar iblis.

An samu Hunter Biden da laifi a tuhume-tuhumen aikata manyan laifuffuka 3 dake da nasaba da saye da mallakar bindiga a lokacin da yake matukar mu’amala da hodar iblis.

Mataimakan alkalin jihar Delaware 12 ne suka samu dan shugaban kasar da laifi a tuhume-tuhumen aikata manyan laifuffuka 3 dake da nasaba da saye da mallakar bindiga lokacin da yake yawan ta’ammali da hodar iblis.

Biyu daga cikin tuhume-tuhumen 3 nada nasaba da bayanan daya cike lokacin da ya sayi bindigar.

Daya daga cikin takardun bayanan na dauke da tambayoyi game da tarihin aikata laifi na mutum, da kuma ko yana sayen bindigar domin amfanin kansa ko kuwa wani ya sayawa da kuma ta’ammali da kwaya da lafiyar kwakwalwa.

Ana tuhumarsa ne da shigar da bayanan karya lokacin da zai sayi bindigar inda yace baya ta’ammali da miyagun kwayoyi tare da yiwa dillalin bindigogi mai lasisi karya.

Dukkanin tuhume-tuhumen 3 manyan laifuffuka ne kuma yana iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 25 da tarar da takai har dala dubu 750.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG