Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Cuba Ya Ziyarci Paparoma


Shugaban Cuba Raul Castro da Paparoma Francis
Shugaban Cuba Raul Castro da Paparoma Francis

Raul Castro ya kai ziyarar godiya ga Paparoma a fadarsa da take Valican sabili da shiga tsakanin kasarsa, wato Cuba da Amurka

Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya kai ziyara fadar Vatican jiya Lahadi, domin godewa Paparoma Francis da kashin kansa, sabili da rawar da ya taka wajen kawo karshen kallon hadarin kaka na tsawon shekaru hamsin tsakanin Amurka da Cuba, abinda da ya sa kasashen suna kokarin sake kulla huldar diplomasiya.

Shugaban kasar Cuban ya gana da Paparoma Francis haifaffen Agentina na tsawon kusan sa’a guda, inda suka tattauna da harshensu na Spaniyanci.

Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika na duniya, shine ya taka muhimmiyar rawa a tattaunawar sirrin da aka yi tsakanin Cuba da Amurka da ta kai ga sanarwar da aka yi a watan Disamban bara cewa, kasashen biyu suna daukar matakin sake bude ofisoshin jakadancinsu a manyan biranen kasashensu, da kuma fadada huldar cinikayya. Fadar Vatican tace Paparoma Francis wanda shine Paparoma na farko daga kudancin Amurka, da kansa ya shiga tsakanin kasashen biyu ya kuma karbi bakuncin wakilan kasashen biyu yayin tattaunawar.

A lokacin da yake barin fadar Vatican, Mr Castro yace, “na godewa Paparoma sabili da abinda yayi”. Daga baya ya kuma yabawa irin basira da kamilci da kuma halayen kwarai na Paparoman.

Fadar Vartican ta ba Mr. Castro lambar girmamawa ta St Martin of Tours, ta fice a fannin kula da gajiyayyu. Mr. Castro ya bayyana niyarsa ta halartar duka taron sujada da Paparoma zai jagoranta idan ya kai ziyara kasar Cuba a watan Satumba, kafin ziyarar da zai kai Amurka da kuma ganawa da shugaba Barack Obama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG