Gwamnatin Najeriya ta ce shugaba Goodluck Jonathan zai tsinke ziyarar da yake yi a k7udancin Afirka, ya koma Abuja, babban birnin kasar, nan take. da isarasa Najeriya, zai gana da manyan jami'an soja da na 'yan sanda, domin sake nazarin harkokin tsaron Najeriya.
Shugaba Jonathan ya juya gida ne a bayan da wasu 'yan bindigar vda ake kyautata zaton na kungiyar Boko Haram ne suka kai farmaki a kan garin Bama dake arewa maso gabashin Najeriya ranar talata, har aka kashe mutane 55, akasarinsu 'yan sanda da ganduroba.
A halin da ake ciki kuma, jami'ai a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce 'ya'yan wata kungiyar asiri a Jihar Nassarawa sun hallaka 'yan sanda su akalla 23 wadanda aka tura domin kamo madugun kungiyar.
'Yan sanda sun bayyana famuwar cewa kungiyar asirin da ake kira Ombatse, ta 'yan kabilar Eggon, tana haddasa tashe-tashen hankula da zub da jini.
A wani labarin kuma, tsohon minista mai kula da harkokin 'yan sanda a Najeriya, Dr. Ibrahim Yakubu Lame, ya fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa irin halin da 'yan sandan Najeriya suke ciki, abin takaici ne, kuma tilas a binciko a hukumta jami'an da suka tura wadannan 'yan sanda zuwa kamo madugun kungiyar asirin ba tare da cikakken shirin yiuwwar fuskantar irin wannan kwanton-bauna ba.
Dr. Lame yace idan ana son samun nasarar tabbatar da tsaro a Najeriya, dole ne sai an gyara tsarin aikin dan sanda, domin bayar da karfi tun daga ofishin 'yan sanda na kasa, watau na gunduma ko DPO, har zuwa sama, maimakon damka dukkan ikon aikin 'yan sanda hannun mutum daya tak, watau sufeto-janar.
Ga cikakken bayanin Dr. Ibrahim Yakubu Lame nan...