Dubban mutane da motoci su na can sun rasa hanyar shigewa ta wannan muhimmiyar hanyar da ta hade sassan arewaci da na gabashin kasar.
Wannan lamari ya samo asali ne daga kisan da aka yi ma jami'an 'yan sanda masu yawa, lokacin da suka yi kokarin kamo shugaban kungiyar asiri ta Ombatse, ta 'yan kabilar Eggon a Jihar Nassarawa, wanda ake zargi da laifin tara makamai da kuma kitsa tashe-tashen hankula.
Jaridun Najeriya sun buga rahotannin dake cewa 'yan sanda har vguda 55 ne aka kashe, kuma adadin wadanda suka mutu gaba daya ya kai 90 a wannan fadan da ya wakana a garin Alakyo.
Jaridun na Najeriya sun ce daga cikin motoci 11 na 'yan sanda da aka tura kamo madugun 'yan kungiyar asirin, motoci biyu ne rak suka komo.
Jami'an Jihar Nassarawa sun ce wannan kungiyar asiri ta Ombatse ta kabilar Eggon, tana sanya 'yan wannan kabila ala tilas su na zamowa membobinta.