A hirar da yayi da Muryar Amurka, Barista Modibbo Bakari, ya fadi cewa kasancewa kotun da’ar ma’aikata da ake kira Code of Conduct Tribunal da turanci na karkashin babban alkalin kotun kolin kasar, zai yi wuya kotun ta yi zaman shari’ar alkalin. Ko da yake dakatarwa da aka yi saboda ana gudanar da shari’a ne ba don an tabbatar da laifinsa ba.
Da yake maida martani akan ko shugaban kasa na da hurumin dakatar da babban alkalin kasa, barista Modibbo yace tabbas shugaba Buhari na da wannan hurumin idan ta kama.
Ya kara da cewa idan har shari’a ta gano bai aikata laifukan da ake zarginsa da su ba, ta yiwu ya iya komawa akan kujerar sa.
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta zargi babban alkalin, Walter Onnoghen da laifin kin bayyana wasu kaddarorin sa bisa doka.
Ga karin bayani cikin sauti na hirar da Saleh Shehu Ashaka yayi da Barista Modibbo.
Facebook Forum