Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Ciyo Bashin Dala Biliyan 1.5 Da Yuro Miliyan 995 Daga Waje


Sanata Ahmed Lawan
Sanata Ahmed Lawan

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da gwamnatin tarayyar kasar karkashin jagorancin shugaba Muhammadu ta gabatar mata a cikin watan Mayun shekarar 2020, na neman rancen dala biliyan biyu da miliyan 700 cikin dala biliyan biyar da miliyan 500 daga waje.

Rancen da gwamnatin Najeriya ke nema daga kasashen wajen sun hada da dala biliyan daya da rabi da gwamnatin za ta nema daga babban bankin duniya, sai yuro miliyan 995 kwatankwacin dala biliyan 1.2 daga wasu hukumomin kasashen waje don biyan wasu bukatun gwamnatin tarayyar kasar da gwamnatocin jihohi.

Idan gwamnatin ta karbi rancen, bashin da ke kan Najeriya zai karu zuwa naira triliyan 32 da biliyan 915 kwatankwacin dala biliyan 84 da miliyan 574, da kididdigar ofishin kula da basussukan Najeriya wato DMO ya wallafa a ranar 31 ga watan Disamban bara.

A cikin basussukan da ake bin Najeriya na naira triliyan 32 da biliyan 915, kashi 37.82 na waje ne, a yayin da sauran kashi 62.18 na cikin gida ne.

Haka kuma, majalisar dattawan ta amince da kasafin kudin shekarar 2021 na hukumar kwastam kan naira biliyan 257 da miliyan 183 da dubu 671 da kwabo 71.

Amincewa da ciyo bashi daga waje din da majalisar dattawan ta yi ya biyo bayan yin nazari da amfani da rahoton kwamitin kula da basussuka na cikin gida da waje, da ke samun jagorancin sanata Clifford Ordia dake wakiltar mazabar Edo ta tsakiya.

Idan ba a manta ba, a cikin watan mayun shekarar 2020 ne shugaba Muhammadu Buhari, ya mika wasikar neman amincewar majalisar dattawa kan ciyo bashi daga waje don daukar nauyin wasu muhimman ayyukan gwamnatin tarayya tare da taimakawa gwamnatocin jihohin da ke fuskantar matsalolin kudi wajen aiwatar da muhimman ayyukansu.

A yayin gabatar da rahoton, jagorar kwamitin kula da basussuka na cikin gida da waje, sanata Clifford Ordia, ya ce za'a nemi dala biliyan daya da rabi daga babban bankin duniya don aiwatar da muhimman ayyukan gwamnatocin jihohi dake fuskantar matsaloli sakamakon tasirin annobar korona bairos, a yayin da za'a nemo yuro miliyan 995 daga wasu kasashen duniya da ma masu ba da rance na kasa-da-kasa.

Wa’adin yarjejeniyar karbo rancen da za'a nema daga babban bankin duniya shekaru 25 ne, wanda kuma ya kumshi kuɗin ruwa na kashi 2.45 cikin 100 a kowace shekara.

Wa’adin wanda za’a karbo daga Bankin shigar da fitar da kayayyaki na kasar Brazil zai kasance na tsawon shekaru 15 da kudin ruwa kashi 2.9 cikin 100, a yayin da shi kuma wanda za'a karbo daga Bankin Deutsche na kasar Jamus mai tsawon shekaru bakwai, tare da kudin ruwa kashi 2.87 cikin dari.

Tun bayan gabatar da bukatar neman majalisar dattawa ta amince da karbo rancen a shekarar 2020 ne ‘yan Najeriya da dama suka yi ta nuna damuwa game da yawaita karbo bashi da gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ke yi.

Wasu 'yan na cewa hakan na nufin Najeriya za ta salwantar da duk wata kima da mutuncin da take da su a matsayin ta na ‘yantacciyar kasa.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Agustar shekarar 2020 da ta gaba ma, sai da aka samu rabuwar kawuna tsakanin yan majalisun tarayyar Najeriya a kan rancen dala bilyan 5.3 don gina layin dogo daga birnin Badun zuwa jihar Kano, sakamakon fargaba kan wasu sharuda da ba'a fahimta ba kuma wasu yan majalisun dattawan kasar suka sha alwashin dakile yunkurin saka kasar cikin tarkon kasar China wajen rancen kudadden.

XS
SM
MD
LG