A Italiya masu gabatar da kara sun bada labarin zasu gabatar da bukata gaban kotu cikin mako gobe na neman a sanya shariyar PM Silvio Berlusconi, kasar cikin sahun wadanda za’a gaggauta sauraro.
Ana zargin PM da biyan wata ‘yar karamar yarinya karuwa domin lalata,da kuma amfani da ikonsa ta yadda bai kamata ba.
Bayan sun gabatar da wan nan bukatar ce wani alkali a birnin Milan zai dauki kwanaki biyar ya duba ko akwai isashen shaidar gurfanadda Mr.Berlusconi.
Masu gabatar da kara suna zargin PM dan shekaru 74 da haifuwa da lalata da wata yarinya ‘yar kasar Morocco mai shekaru 17 da haifuwa wacce take aiki a wani Club lokacinda ta ziyarci gidansa.
Dukkansu biyu sun musanta zargin,kodashike yarinyar wacce sunanta ta yanka Karima El-Mahroug an biyata dala dubu tara domin ta halarci liyafar da aka shirya a gidan PM.