Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar NCP Ta Jagoranci Zanga-Zanga A Lagos


Kungiyoyi 7 karkashin jam'iyyar NCP sun yi gangamin nuna rashin jin dadin rashin wutar lantarki a Najeriya

Wasu kungiyoyi guda 7 karkashin jagorancin jam'iyyar National Conscience Party, NCP a takaice, sun gudanar da macin bayyana rashin jin dadinsu kan yadda aka kasa samun wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya.

Masu zanga-zangar sun yi maci trun daga gidan marigayi Cif Ganio Fawehinmi, har zuwa babban ofishin kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya, su na tafe su na rera wakokin nuna kaicon rashin wutar lantarki a kasar.

Masu zanga-zanagr suka ce babu wata kasa a duniya da zata iya samun ci gaba har ta bunkasa ba tare da ta samu wadatacciyar wutar lantarki ba.

Suka ce sun gaji da yadda ake gallazawa rayuwar 'yan Najeriya a saboda rashin lantarki, kuma a duk wata sai an kawo musu takardun biyan kudin lantarkin da bai biya musu bukata ba.

Shugaban jam'iyyar NCP na kasa, Dr. Yunusa Tanko, wanda ya jagoranci zanga-zangar, yace ba yin maganganu kan shugaba Jonathan ko Atiku Abubakar ko Buhari ne kawai siyasa ba, tilas ne suyi magana kan abubuwan da jama'a ke bukata kamar wutar lantarki domin ita zata inganta rayuwarsu.

Ga cikakken rahoton Ladan Ibrahim daga Lagos kan wannan zanga-zanga.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG