Tun Wani babban balan-balan da ke yawo a sararin samaniyar Amurka ya haifar da cece-kuce a harkokin diflomasiyya, kuma ya janyo muhawarar tsakanin banbancin ra’ayoyi a shafukan sada zumunta.
Kasar China ta dage kan cewa jirgin balan-balan din na wani kamfani mai zaman kansa ne, da ake amfani da shi don tattara bayanan Yanayi, iska ce ta ja shi zuwa sararin samaniyar Amurka bisa kuskure sabodsa ba ya iya sarrafa kansa sosai.
Sai dai Amurka ta ce ba tare da kokwanto ba, balan-balan din na leken asirin kasar China ne. Gano wannan jirgi ya sa sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, soke ziyarar da zai kai kasar China a karshen mako da nufin kawar da tashe-tashen hankula da suka yi kamari a tsakanin kasashen.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta ce jirgin balan-balan din ya na dauke da na'urori masu auna firikwensin da na'urorin sa ido, ya nuna alamun yana iya sarrfa kansa da inda yake nufa.
Jirgin ya yi ta zagaye a wasu yankuna masu muhimmanci na garin Montana, inda aka lullube makaman nukiliya, lamarin da ya sa sojoji suka dauki matakin hana ta tattara bayanan sirri.
Wani mai magana da yawun Pentagon, ya ce jirgin zai iya kasancewa a sararin samaniyar Amurka na "yan kwanaki," ya kuma nuna rashin tabbas game da inda jirgin zai dosa, ko kuma idan Amurka za ta yi kokarin kwace shi ba tare da tashin hankali ba.
Kuma da yammacin ranar Juma'a, ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta amince da rahotannin wani jirgin balan-balan na daban da ke shawagi a yankin Latin Amurka - wanda aka kiyasta a matsayin "wani jirgin balan-balan liken asiri na kasar China."