Kungiyoyin agaji na kasa da kasa da ta Niger sun bayyana damuwarsu akan yadda matsalar tsaro ke kawo masu cikas akan gudanar da ayyukansu. Sun baiyana haka ne wajen wani taron yan jarida na hadin gwiwa.
Matsalar ta fi kamari a garuruwan dake fama da yawan tashe tashen hankula kamar wadanda suke makwaptaka da tafkin Chadi da kuma wadanda suke kan iyaka da kasar Mali da Burkina Faso.
Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa a Jamhuriyar Niger y ace abun da ya fi mahimmanci shi ne yadda zasu iya kasancewa kusa da al’umma dake cikin hali na tsaka mai wuya sakamakon jibge jami’an tsaro.
A kasashe kamar Mali akwai jami’an tsaro na kasashen waje da na kasar da kuma ‘yan ta’adda dake dauke da makamai dukansu suna kawowa aikin agaji cikas. Suna bukatar su kasance da jama’ar dake bukatar daukin gaggawa.
Wata matsala da kungiyoyin ke fuskanta, kuma ita ce ta bakin haure, domin kwana kwanan nan kasar Niger ta karbi bakin haure daga kasashen Eritrea da Habasha da Sudan.
Ali Bange, shugaban kungiyar agaji a Jamhuriyar Niger yace suna taimakawa bakin hauren wajen yi musu jinya da kai su asibiti. Suna kuma taimakawa mata masu yara kanana da abinci da neman masu hanyar da zasu koma kasashensu.
Kimanin mutane dubu bakwai ne suka rasa aikinsu a sakamakon hana safarar bakin haure. Yace wadannan mutanen su ne suke daukan bakin haure suna kai sukasashen waje amma yanzu an hana saboda haka suna nan kara zube. Sun zama babbar matsala a garin Agades.Ya kamata a samar musu aiyukan yi, domin kada su shiga wani hali.
A saurari rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani
Facebook Forum