Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Rohingya Sun Yi Zanga-zanga


Zanga-zangar 'yan kabilar Rohingya
Zanga-zangar 'yan kabilar Rohingya

Ganin irin ukubar da aka gana masu, 'yan kabilar Rohingya na kasar Myanmar sun yi zanga-zangar nuna alhininsu kan zagayowar ranar da hukumomin kasar su ka murkushe tare da kashe su da dama, musamman ma a jahar Rakhine.

Dubban ‘yan gudun hijirar Rohingya sun yi zanga-zangar alhinin zagayowar shekarar da kasar Myanmar ta murkushe wannan karamar kabila, al’amarin da ya tilasta su gudu zuwa kan iyaka da kuma cikin kasar Bangladesh, abin da ya kai ga kafa sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya.

Masu zanga-zangar sun yi gangami tare kuma da addu’o’i jiya Asabar a sansaninsu na ‘yan gudun hijira da ke Cox Bazar, na neman a yi adalci ga Musulmi tsiraru. Jami’ai na kasa da kasa dai sun bayyana murkushe ‘yan Rohingya da hukumomin Myanmar su ka yi a jahar Rakhine, da kisan kare dangi.

Ita kuma gwamnatin Myanmar ta bayyana murkushewar da matakin tsaro da ya wajaba don taka burki ma mayakan Musulmi. Kasar ta Myanmar ta ce yanzu yanayi ya kyautatu ta yadda ‘yan gudun hijirar za su iya komawa gida, ikirarin da ake dari-dari da shi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG