Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Menene Dalilin Baiwa Ali Modu Sheriff Kariya?


Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya.

A cikin firar da yayi da Muryar Amurka tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jam'iyyar APC Dr. Haruna Yerima ya nuna shakku kan baiwa tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sheriff Kariya.

Dr. Haruna Yerima yace ya gayawa hafsan sojojin Najeriya Janaral Minima ya fito ya yiwa 'yan Najeriya bayanin dalilan da suka sa yana baiwa Ali Modu Sheriff kariya.

Inji Dr. Haruna Yarima hafsan yana anfani da sojoji da manya manyan kayan yaki ya je ya tarbi tsohon gwamnan jihar a filin saukar jiragen sama duk lokacin da ya je Maiduguri. Menene dalilin yi masa haka. Shin domin kudi ne ko mukami ko kuma domin shi tsohon gwamna ne. Idan domin yana tsohon gwamna ne akwai tsoffin gwamnoni uku da suke da rai a jihar.

Tsohon gwamna Muhammed Gwoni yana yawo da tsohuwar motarsa. Da ita ake kaishi Abuja kuma ko dansanda daya bashi dashi. Akwai Maina Ma'aji da Sharma duk babu wanda ya san da zamansu. Sabili da haka Janaral Minima ya gayawa kasar dalilin da ya ke baiwa Modu Ali Sheriff kariya.

Dr. Haruna Yarima yace idan Janaral Minima bai basu amsa ba cikin dan lokacin da suka bashi zasu garzaya kotu.

Amma tsohon kwamishanan yada labarai na jihar Borno Inuwa Bwala yace a hadu a kotun domin kowane dan Najeriya sananne idan zashi Maiduguri ana bashi jami'an tsaro sabili da halin da kasar ke ciki. Irin tsaron da ake baiwa Modu Sheriff ana iya ba kowa ma.

Imrana Wadana shugaban cigaban matasan arewa ya ce lalacewa ce irin ta mutanen kasa ta jawo haka. Modu Sheriff tsohon gwamna ne amma ina ya samu irin kariyar da ake bashi wadda ba'a ba gwamnan yanzu irinta. Gwamna mai ci yanzu bashi da kariya. Haka ma Sanata Ali Ndume. Shi wanene illa dai yana biya wa wadanda ke ta'adanci bukatunsu shi yasa yake zaune lafiya.

Mark Amani shugaban kananan kabilun arewa yace 'yancin Ali Modu Sheriff ne a bashi kariya.

Ga rahoton Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG