Tun lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya fada cewa zai mayarda hekwatar rundunar sojoji Maiduguri har sai an ga bayan kungiyar Boko Haram aka samu karin hare-haren bamabamai da kunar bakin wake.
Lamarin ya sa jama'a da dama suna cigaba da nuna goyon bayansu da yunkurin kawo masu hekwatar sojojin. To amma jama'a na ganin idan an kawo hedkwatar Maiduguri to a tura sojojin zuwa cikin daji inda 'yan ta'adan suka yi kakagida domin a fuskancesu gadan gadan. Jama'a na ganin barin sojoji cikin gari ba zai haifi da mai ido ba.
Jama'a sun tunawa shugaban kasa abubuwan da ya kamata ya kula dasu. Alhaji Ibrahim Guldi daya daga cikin dattawan jihar yace yunkurin zai yi kyau. Ya tuna lokacin da shi shugaban kasa yake kwamandan rundunar sojoji ta uku a Jos yadda ya murkushe wani yunkurin da 'yan Chadi suka yi na mamaye wani yankin Najeriya. Abun da yake son yayi ke nan yanzu domin a kakkabe 'yan ta'ada gaba daya.
Wani matashi Malam Usman Agoni yace furucin shugaban kasa ya dace amma ya kirashi ya yi la'akari da wani abu guda. Yace kada a kuskura a bar sojoji cikin Maiduguri. A turasu daji inda 'yan ta'adan suke ta haka za'a ci nasara. Su shiga dajin Sambisa su yakesu. Yace duk inda suke a shiga a nemesu. Yace duk wanda aka ce ana nemansa hankalinsa ba zai kwanta ba balantana ya samu lokacin shirya kai hare-hare.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.